Alhamis 6 Maris, 2025 da 3:47:46 Safiya
Ƴan Najeriya na ci gaba da kokawa kan yadda bankuna ke ci gaba da yanke musu kuɗi a duk lokacin da suka ciri kuɗi ko suka tura kuɗin zuwa wasu bankuna.
__
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/03/2025
Alhamis 6 Maris, 2025 da 3:33:27 Safiya
Liverpool na farautar ɗan wasan Bournemouth mai shekara 21 daga Hungary Milos Kerkez kan fam miliyan 40.
Alhamis 6 Maris, 2025 da 3:50:03 Safiya
Sheikh Dr Jabir Maihula wanda malamin addinin Musulunci ne a jihar Sokoto, ya lissafa wasu abubuwa biyar da mutane ke tunanin na karya azumi amma sam ba su karya azumin.
Alhamis 6 Maris, 2025 da 6:22:35 Safiya
Shugaba Trump ya bukaci Hamas ta gaggauta sakin dukkan mutanen da take garkuwa da su a Gaza
Alhamis 6 Maris, 2025 da 3:51:28 Safiya
Mako biyu kenan tun bayan da M23 ta ƙwace iko da birnin Bukavu. Mazauna yankin sun faɗa wa BBC cewa mutane na cike da fargaba.
Laraba 5 Maris, 2025 da 2:10:16 Yamma
Sanata Natasha Akpoti Uduaghan, ƴar majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar jihar Kogi ta gabatar da ƙorafi a gaban majalisar dattawan ƙasar kan shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio.
__
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 05/03/2025
Laraba 5 Maris, 2025 da 6:16:41 Yamma
La'akari da halayyar Trump kan tsare-tsare da manufofi da kuma furucinsa tun bayan da ya hau mulki a watan Janairu - musamman yadda ya sake karɓar Shugaban Rasha - ko za a iya cewa tsarin aƙidar Sassaucin Ra'ayi na haɗinkai da bin doka ya kama hanyar mutuwa?
Laraba 5 Maris, 2025 da 10:19:25 Yamma
Benfica ta yi rashin nasara 1-0 a hannun Barcelona a wasan farko zagayen ƴan 16 a Champions League da suka kara ranar Laraba.
Laraba 5 Maris, 2025 da 11:35:02 Yamma
Liverpool ta je ta yi nasara a kan Paris St Germain da cin 1-0 a wasan farko zagayen ƴan 16 a Champions League ranar Laraba a Faransa.
Laraba 5 Maris, 2025 da 4:10:51 Yamma
Da ƙyar idan Arsenal za ta ɗauki Premier League na bana, amma tana turbar lashe Champions League in ji Thierry Henry.
Laraba 5 Maris, 2025 da 3:27:12 Yamma
Watakila Harry Maguire da Manuel Ugarte ba za su buga wa Manchester United wasa da Real Sociedad ba ranar Alhamis a Europa League.
Laraba 5 Maris, 2025 da 2:45:35 Yamma
Fede Valverde ya buga wa Real Madrid wasa na 300 a karawar da suka yi nasara kan Atletico a Champions League ranar Talata.
Laraba 5 Maris, 2025 da 10:35:24 Safiya
Sun amince da tsarin ne a wani taron gaggawa da suka gudanar a Alkahira, babban birnin Masar.
Laraba 5 Maris, 2025 da 10:43:23 Safiya
Rana ce wadda za ka ga ana shafa toka a goshi, wannan toka da ake shafawa a goshi alama ce ta tuba da neman gafara da neman nufin ubangiji a cikin rayuwa na wadan nan kwanaki masu tsarki guda 40.
Alhamis 27 Faburairu, 2025 da 11:59:00 Safiya
Wannan shafi ne da ke sanar da masu sha'awar girke-girke ƙa'idojin aiko wa da BBC bidiyon girke-girken Ramadan na 2025 tare da kuma yadda za ku aiko da bidiyon naku.
Laraba 5 Maris, 2025 da 3:57:12 Safiya
Sabon rahoton na 2024 ya ce "kashi 51 na dukkan mace-macen da ta'addanci ya haifar" sun faru ne a Sahel - ma'ana 3,885 na jimillar 7,555 da aka samu a faɗi duniya.
Laraba 5 Maris, 2025 da 3:55:19 Safiya
Waɗannan ƴan siyasa dai ana kiransu da suna 'Sojojin Baka' suna shiga gidan radiyo ta cikin wasu shirye-shiryen siyasa suna suka ko yabon gwaninsu a siyasance kuma wasu lokutan ba tare da la'akari da abin da ka-je-ya-zo ba.
Talata 12 Maris, 2024 da 4:20:05 Safiya
Kasancewar addinin Musulunci cike yake da sauki ya sa bayan wajabta azumin Ramadan Sai kuma aka zayyana wasu mutane da kodai aka daukewa azumin Kwata-kwata ko kuma na wucin gadi.
Talata 4 Maris, 2025 da 5:51:23 Yamma
Zango na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta kasance cikin rashin tabbas, kuma a yanzu al'amarin ya fito fili inda alamu ke nuna babu ita a daidai lokacin da ake sa ran za ta fara aiki.
__
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya, Talata - 04/03/2025
Talata 4 Maris, 2025 da 10:49:13 Safiya
Bayan da matatar man fetur ta Dangote ta sanar da rage farashin litar man fetur zuwa naira 825 ga dillalai, a farkon makon nan shi ma kamfanin NNPC ya rage nasa farashin zuwa naira 840 a Legas.
Talata 4 Maris, 2025 da 6:48:18 Yamma
A tsakanin 2020 da 2023, ƙiyasi ya nuna cewa an samu kimanin mata dubu 16 a ƙasashen da ke yankin gabashin Afirka, na zuwa a yi musu irin wannan tiyata, a cewar ma'aikatar Lafiya a Kenya.
Talata 4 Maris, 2025 da 3:57:06 Safiya
Direbobin sun ce an kashe ƴan'uwansu da dama tare da ƙona kayan da suka dauko da ma ɗaruruwan motocinsu.
Talata 4 Maris, 2025 da 1:22:38 Yamma
Matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya ɗauka na dakatar da bayar da tallafin soji ga Ukraine babban abin damuwa ne ba ga Ukraine ɗin kawai ba, har ma da ƙawayenta na nahiyar Turai waɗanda suke ta bibiyar Amurkar domin shawo kanta ta ci gaba da taimakon da take yi.
Talata 4 Maris, 2025 da 12:39:10 Yamma
Masu binciken sun yi gargaɗin cewa ƙaruwar teɓa za ta hauhawa cikin sauri a ƙarshen shekaru goman da muke ciki, musamman a ƙasashe masu ƙarancin arziki.
Talata 4 Maris, 2025 da 3:56:41 Safiya
Sheikh Daurawa ya ce abin da ake kira azumi dama shi ne kamewa daga ci da sha da mu'amalar aure da duk abubuwan da ke karya azumi tun daga ketowar alfijir zuwa zuwa faɗuwar rana.
Talata 4 Maris, 2025 da 3:58:00 Safiya
Tsawon shekaru, ƙungiyar PKK na gwabza yaƙi da dakarun Turkiyya domin kafa ƙasar Kurdawa a Gabas ta Tsakiya.
Litinin 3 Maris, 2025 da 5:17:44 Yamma
"Ba a cikin jami'ar ake satar ɗalibai ba. A unguwannin da suke zaune ne a nan ƴanbindigar ke zuwa su sace su. Saboda mazaunin jami'ar na dundundun da ke wajen garin Dutsin-Ma ba zai zaunu ba saboda matsalar tsaro." In ji wani malamin jami'ar da bai so a ambaci sunansa ba.
__
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sassan duniya kai tsaye, na Litinin, 03/03/2025
Litinin 3 Maris, 2025 da 3:58:46 Yamma
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya koma gida Kyiv bayan balaguron da ya yi na kwana uku bayan ɓaɓatun da suka yi da Donald Trump da mataimakinsa JD Vance.
Litinin 3 Maris, 2025 da 11:36:04 Safiya
A wannan karo iyalai da dama sun samu damar haɗuwa domin yin buɗe-baki a tare, wani abu da ba su samu damar yi ba tun shekarar 2023.
Lahadi 2 Maris, 2025 da 12:02:37 Yamma
Wannan labari na Naɗin Lauje yana jan hankali ne a kan muhimmancin gwajin jini kafin aure.
Lahadi 2 Maris, 2025 da 12:19:36 Yamma
A filin na wannan mako za ku ji ko bayanin likita game da abin da ke jawo ciwon kai na ɓari ɗaya wato migrane, da amsoshin wasu tambayoyin.
Asabar 1 Maris, 2025 da 11:38:50 Safiya
Lafiya Zinariya: Ko kin san matsalar da kan shafi jakar ƙwayayen mace?
Asabar 1 Maris, 2025 da 9:31:51 Safiya
Majalisar Ƙoli ta harkokin Shari'ar Musulunci ta Najeriya ce a ƙarƙashin shugabancin Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III ta nemi a samar da dokokin da za su tantance masu wa'azi, lamarin da ya ja hankalin mutane.
Jummaʼa 8 Disamba, 2023 da 6:50:55 Yamma
Sashen Hausa na BBC na watsa shirye-shirye guda huɗu a kowace rana, na tsawon minti talatin-talatin cikin harshen Hausa.